Search
Close this search box.

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya gana da Sarkin Qatar

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Arif ya gana a yau Juma’a a birnin Doha tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad inda

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Arif ya gana a yau Juma’a a birnin Doha tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin da ma duniya baki daya.

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Arif ya isa kasar Qatar domin halartar jana’izar shahid Ismail Haniyya.

Kafin ya tafi Qatar don halartar jana’izar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Riza Arif ya bayyana cewa sakon al’ummar Iran da juyin juya halin Musulunci na Iran shi ne hadin kai da al’ummar Palastinu da ake zalunta, da kuma mara baya ga manufofinsu halastattu, masu alaka da ‘yantar da Kudus.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments