Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.”
Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.”
Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Mista Khalaf ya jaddada “dangantaka ta zahiri” tsakanin Gaza, yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye da kuma gabashin al-Quds, yana mai cewa suna wakiltar “yankin kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma dole ne su kasance karkashin cikakken ikon mallakar Falasdinawa da gudanar da mulki.”
A ranar Talata ne, Yair Lapid na Isra’ila ya gabatar da wani shiri na Gaza bayan kawo karshen yakin.
A karkashin shirin nasa, Masar za ta karbi ragamar tafiyar da yankin da zarar an kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
“Mafita ita ce Masar za ta dauki nauyin gudanar da Zirin Gaza na tsawon shekaru takwas tare da zabin tsawaita shi zuwa shekaru 15,” kamar yadda ya shaida wa kungiyar Haukish Foundation for Defence of Democracy (FDD) a Washington.