Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da sanarwa da a ciki ta bukaci Isra’ila da ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon tana mai cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci.
Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Badar Abdulatif ya ce, wajibi ne ga Isra’’ila da ta janye sojojin nata daga Lebanon ba tare da wani sharadi ba, domin ba za a kyale ta akan koda taku daya na kasar Lebanon ba.
A karkashin sharadin tsagaita wutar yaki da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024, Isra’ila za ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Lebanon a ranar 26 ga watan nan na Janairu.
Ya zuwa yanzu dai an tura sojojin Lebanon da kuma na MDD a cikin garuruwan dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya,sai dai duk da hakan HKI tana ci gaba da zama a cikin wasu gargruwan na wannan yankin.
A makon da ya shude ne dai Amurka da kuma gwamnatin Lebanon su ka karawa Isra’ila wa’adin zuwa 18 ga watan Fabrairu domin su janye daga kasar.
Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya ce, ci gaba da zaman sojojin HKI a cikin Lebanon ya sabawa doka, kuma babu wani dalili da zai sa ta rika kai wa farafen hula hare-hare.