Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila.
Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu.
Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar.
Bugu da kari Masar din ta sanar da cewa ta tuntunbi sauran kasashen larabawa da kuma gwamnatin Falasdinu, domin tattauna batutuwa masu hatsari da su ka bijiro akan batun Falasdinu.
A gefe daya, Masar din ta sanar da cewa, ministanta na harkokin waje Badar Abdul-Adhi, ya nufi kasar Amurka domin tattaunawa da mahukuntanta.
Shirin yin wannan taron na kungiyar kasashen larabawa ya zo ne bayan wani furuci da shugaban kasar Amurka ya yi na ganin Falasdinawa sun yi hijira daga Gaza, zuwa kasashen Masar da Jordan.
Donald Trump na Amurka ya bayyana aniyarsa ta yin manyan gine-gine a cikin zirin Gaza, bayan ficewar Falasdinawa da kuma karbar yankin da Amurka za ta yi daga hannun HKI.
Tuni dai shugaban na kasar Amurka ya fara fuskantar suka daga bangarori mabanbanta.