Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar.
Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma maido da tsaro a fadin kasar.
Ta kara da cewa, “Masar ta bukaci dukkan sojojin Sudan da su ba da fifiko ga cin moriyar kasa mafi girma da kuma taka rawar gani wajen bullo da wani cikakken tsari da zai kawo hadin da daidaito ba tare da nuna banbanci ko tsoma bakin kasashen waje ba.”
Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef al-Sharif ya tabbatar a karshen watan da ya gabata cewa “babu wanda zai amince da abin da ake kira gwamnatin hadaka a Sudan, kuma babu wata kasa da za ta amince da ita.