Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da Shugaban Eritrea Isaias Afwerki domin tattauna halin da ake ciki a yankin,  Shugaba al-Sisi ya tabbatar da

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da Shugaban Eritrea Isaias Afwerki domin tattauna halin da ake ciki a yankin,  Shugaba al-Sisi ya tabbatar da jajircewar Masar wajen tallafawa ‘yancin kai da kuma ‘yancin yankin Eritrea.

A yayin taron, wanda Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty da takwaransa na Eritrea, Osman Saleh Mohammed suka halarta, shugabannin biyu sun tattauna halin da ake ciki a yankin.

Sun tabbatar da hangen nesansu kan hanyoyin kawo karshen yakin a Sudan, suna masu  jaddada bukatar tallafawa cibiyoyin gwamnati na kasa, musamman Sojojin Sudan, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na kafa hukumomi ko cibiyoyi  masu kishiyantar gwamnati a kasar.

Shugaba al-Sisi ya jaddada matsayar Masar da kuma  kokarin da take yi  don kawo karshen yakin da kuma rage wahalhalun jin kai na al’ummar Sudan, ta hanyar yin aiki tare da abokan huldar Masar  don tabbatar da hadin kan Sudan, mutuncin yankin, da kuma ‘yancin kan kasa.

A nasa bangaren, Shugaba Afwerki ya nuna matukar godiyarsa ga rawar da y ace Masar tana  takawa karkashin jagorancin Shugaba El-Sisi, wajen karfafa zaman lafiya da kuma kokarin ci gaban  yankin kusurwar Afirka da Gabashin Afirka. Ya yi maraba da fadada hadin gwiwar tattalin arziki da Masar da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan batutuwan kasa da kasa da na yanki masu amfani ga junansu.

Taron ya kuma yi magana kan sabbin abubuwan da suka faru a Somaliya, inda Shugabannin biyu sun jaddada kudurin kasashensu na amincewa da sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a taron kolin Masar, Eritrea, da Somaliya a Asmara a watan Oktoban 2014, wanda ya tabbatar da wajibcin girmama ka’idoji da dokokin kasa da kasa, musamman ma cikakken yankin Somaliya da dukkan kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments