Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya tattauna da takwaransa na Saudiyya, Laftanar Janar Fayyad bin Hamed al-Ruwaili, kan hanyoyin inganta diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya.
Tun da farko kanfanin dillancin labaran Iran Tasnim ya bayyana cewa al-Ruwaili yana jagorantar wata babbar tawagar sojojin Saudiyya a ziyarar da ya kai birnin Tehran.
A shekarar da ta gabata, Bagheri ya tattauna ta wayar tarho da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman, inda suka mai da hankali kan halin da ake ciki a yankin, da inganta hadin gwiwar tsaro tsakanin sojojin kasashen Saudiyya da Iran, da kuma tinkarar muhimman batutuwan da suka shafi kasashen musulmi.
Hakan ya biyo bayan dawo da huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu ne a watan Maris din shekarar 2023.
A watan Oktoba ne Saudiyya ta sanar da gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa tare da Iran da sauran kasashe a tekun Oman.
Haka nan kuma Iran ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani da kuma sasanta Yemen da Saudiyya, wanda hakan ya kawo karshen yakin da aka kwashe tsawon shekaru ana gwabzawa tsakanin Saudiyya da Yemen.
Saudiyya da Iran sun gudanar da tattaunawa domin daukar matakai na hadin gwiwa domin ganin an dakile ruruwar wutar yaki a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda Saudiyya ta sheda wa Amurka da Isra’ila cewa ba za ta taba bari a yi amfani da sararin samaniyarta ko wani na kasarta domin kaiwa kasar Iran hari ba.
Kasashen Iran da Saudiyya suna muhimmanci a yanki, ta yadda hadin kai da hadin gwiwa a tsakaninsu zai iya zama babban karfe kafa da zai hana kasashe masu girman kai cimma manufofinsu a gabas ta tsakiya da kuma kasashen larabawa da na musulmi.
Baya ga haka kuma irin wannan hadin gwiwa tsakanin Iran da Saudiyya zai taimaka matuka wajen kaera kusanto da musulmi da hada kansu wuri guda, tare da yin abin da ya rataya a kansu a matsayinsu na al’umma guda.