Search
Close this search box.

Manya Manyan Jami’an Sojojin Ruwa Na Iran Da Afirka Ta Kudu Sun Gana A Iran

Manya manyan kwamandojin sojojin ruwa na kasashen Iran da Afirka ta Kudu sun gana a jami’ar sojojin ruwa na Imam Khomaini(q) da ke Noshahr na

Manya manyan kwamandojin sojojin ruwa na kasashen Iran da Afirka ta Kudu sun gana a jami’ar sojojin ruwa na Imam Khomaini(q) da ke Noshahr na kudancin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Afirka ta kudu Admiral Munde Lobse ya gana da tokwaransa na kasar Iran Admiral Shahram Irani da kuma Janar Alireza tangsiri kwamanda na sojojin ruwan a rundunar IRGC.

Labarin ya kara da cewa Admiral Munde Lobse dai, kafin haka ya ga kataparen jirgin ruwan yakin da kasar Iran ta gina mai suna ‘Dana’ a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu a lokacinda ya yada zango a tafiyar zagaya duniyan da yake yi a lokacin wanda ake kita ‘Tafiya Ta 86’.

Bayan zagayawa da yayi a cikin jami’ar Imam Khomani(q) na tarbiyyar sojojin ruwa na kasar Iran, Admiral Munde Lobse ya bukaci karfafa dangantaka da kasar Iran a bangarori daban daban na sojojin ruwan kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments