Manya-Manyan Jami’an Gwamnatin Amurka Sun Isa Kasar Siriya Don Tattaunawa Da HTS

Manya-manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka sun isa birnin Damascus babban birnin kasar Siriya don tattauna da yan ta’adda shuwagabannin kungiyar HTS wadanda ta taimakawa wajen

Manya-manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka sun isa birnin Damascus babban birnin kasar Siriya don tattauna da yan ta’adda shuwagabannin kungiyar HTS wadanda ta taimakawa wajen kifar da gwamnatin Bashar Al-asad.

Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka na fadar haka, ya kuma kara da cewa, Jami’an gwamnatin Amurka zasu ji ta bakin shuwagabannin yan ta’adda na kungiyar Hai’atu Tahririn Sham, sannan su ga ta yadda za su taimaka masu su tafiyar da al-amuran shugabancin kasarsu.

Tawagar manya-manyan jami’an gwamnatin kasar ta Amurka dai sun hada da babban Jami’ii a ma’aikatar harkokmin wajen kasar mai kula da yammacin Asiya Barbara Leaf da kuma Daniel Rubinstein shima daga ma’aikatar wanda kuma aka bashi aikin kula da al-amuran kasar Siriya bayan faduwar gwamnatin shugaba Asad.

Wannan labarin yana zuwa ne kimani mako guda kenan da sanarwan da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayar na cewa gwamnatin Amurka tana tattaunawa kai tsaye da shuwagabn kungiyar yan ta’adda ta HTS wadanda suke iko da kasar Siriya tun bayan faduwar Al-Asad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments