Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya  

Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata

Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba

Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma duk wani sabon harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci azamar mayar da martani daban da na baya.

Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada matsayin wadanda suka yi shahada a safiyar yau Alhamis a yayin bikin tunawa da ranar shahidan Iraniyawa a hare-haren wuce gona da iri, yana mai daukar su a matsayin ginshikan tabbatar da tsaron kasar Iran a yau da gobe.

Manjo Janar Mousavi ya ce: “Taron tunawa da shahadar wadannan kananan yara, da kumajin al’ummar Iran – tun daga jarirai da yara zuwa malamai, masu ceto, ‘yan jarida, likitoci, shugabanni, da sauran kungiyoyi – ya zo daidai da ranar Arba’in na shugaban shahidai Jagoran al’umma Abu Abdullah al-Hussein {a.s} yana ci gaba da nuna al’adar wannan al’umma a cikin tarihin Ashura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments