Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji.
Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan.
A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya.
Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.