A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai
Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso.
Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83.
Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.”
Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara gudanar da bincike akan zubin sabbin sanadarorin na magani a cikin dakunan bincike, kuma a karshe mu ka yi nasara.
Haka nan kuma ya ce; A karon farko a cikin Iran mun samar da sanadarin mafi muhimmanci na hada wannan maganin a cikin gida wanda kuma ya kai ga yinsa cikin kwayoyi da kafso.