Wata kotun kasar Mali ta kori karar da aka shigar a gabata, don neman soke matakin da majalisar soj0jin kasar ta dauka na rusa jam’iyyun siyasa gaba daya.
A ranar 13 ga watan Mayu ne da ya gabata ne majalsiar koli ta sojojin kasar Mali ta fitar da dokar haramta dukkan jam’iyyun siyasa a kasar wadanda yawansu ya kai 300, tare da manusar sake fasalinsu.
Wasu lauyoyi da kuma ‘yan siyasar kasar ne dai su ka shigar da karar a gaban kotu, daga cikinsu har da ‘Montagal Tal’ wanda ya kasance jagoran daya daga cikin jam’iyyun da aka majalisar sojojin ta soke.
Masu shigar da karar, sun bayyana matakin da majalisar sojan kasar ta dauka da cewa keta hurumin ‘yancin siyasa ne da kuma yencin yin taruka.