Mali : An rushe dukkan jam’iyyun siyasa a hukumance

A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata,

A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance.

bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar.

An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi.

Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa.

Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments