Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya

Wani tsohon dan majalisar kasar labanon ya bayyana cewa kasarsa ba ta bukatar wata yarjejeniya da zaa kulla kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar

Wani tsohon dan majalisar kasar labanon ya bayyana cewa kasarsa ba ta bukatar wata yarjejeniya da zaa kulla kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da hki take yi , kana yayi gargadin cewa makircin da aka kulla kan kasar siriya aka kai ta kasa irinsa ne ake  kullawa akan kasar labanon,

Hussain haj Hassan yace babu wani amfani kara tattaunawa kan  wata yarjejeniya da isra’ila tun da ta kasa tsayawa ta yi aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan nuwambar shekarar da ta gabata.

Daga karshe ya nuna cewa gwamnatin dake rike da kasar siriya ta haiati tahrir al sham abokiyar Amurka ce don haka har yanzu isra’ila na ci gaba da wuce gona da iri a yankuna daban daban na kasar siriya gaba gadi,

Yace gwargwadon yadda ka bawa makiya dama gwargwadon yadda zaka kara yin rauni a gabansu,  don haka hizbullah da hadin kan kasa su ne kawai wanda za su bada garanti kan tsaro da zaman lafiyar kasar labanon

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments