Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran.
Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran.
Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha.
Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a fannin mai da iskar gas, da kuma raya ayyukan hadin gwiwa na dogon lokaci a fannin makamashin nukiliya cikin lumana.
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan dai kasashen Iran da Rasha, sun kara karfafa hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban, duk kuwa da tsauraran takunkumin da kasashen yamma suka kakaba musu.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke kara ruruwa, sakamakon barazanar yaki da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan Iran idan har Tehran ta gaza cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya.