Majalisar dokokin Sloveniya za ta kada kuri’a domin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.
An shirya zaman ne ranar Talata mai zuwa in ji shugaban majalisar Sloveniar, Urska Klakocar Zupancic, a wani taron manema labarai a ranar Alhamis.
Idan matakin ya samu amincewa da kasar Falasdinu a hukumance, Slovenia za ta bi sahun kasashen Spain, Ireland da Norway, wadanda suka amince a hukumance da falasdinun a mastayin kasa a ranar Talata daga gabata.
Kasashen uku na turai uku da suka hada da Spain da Ireland da Norway sun sanar da cewa sun amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Duk da matsin lambar da Isra’ila ta yi da kuma kin amincewar Amurka, kasashen Turai uku sun amince da Falasdinu a matsayin kasa.