Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ce za su gana da bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a birnin Geneva,

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ce za su gana da bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a birnin Geneva, sai dai shugaban bai bayyana  ranar da za a yi wannan tattaunawar ba.

Guterres ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da kafar talabijin ta Al Arabiya da ke Saudiyya wadda ta tattauna da shi game da yunkurin da majalisar ke yi ba ganin an sasanta rikicin na Sudan.

Sai dai Tattaunawar na zuwa ne a dai dai lokacin da mayakan RSF ke ci gaba da kwace yankuna a cikin kasar tare da kisan fararen hula da dama, da kuma tilastawa miliyoyin barin matsugunansu.

Tun a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023 ne yaki ya barke tsakanin dakarun Sojin Sudan karkashin Janar Abdelfattah al-Burhan da kuma dakarun kai daukin gaggawa na RSF karkashin Muhmmad Hamdan Dagalo ,rikicin da ya juye zuwa yaki mafi muni da kasar ta gani a tarihi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted