MDD za ta kada kuri’a kan daftarin kudurin tsagaita wuta a Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a kan daftarin kudiri da ke neman dakatar da bude wuta cikin gaggawa, ba tare da sharadi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a kan daftarin kudiri da ke neman dakatar da bude wuta cikin gaggawa, ba tare da sharadi ba, kuma na dindindin a dukkan bangarorin yankin Zirin Gaza, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa Al Mayadeen.

Majiyoyin sun bayyana cewa daftarin kudurin ya sake nanata bukatar Majalisar na sakin dukkan wadanda ake tsare da su ba tare da wani sharadi ba, kuma ya ki amincewa da duk wani yunkuri na kashe al’ummar Palasdinu da yunwa.

Kudurin ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar  da muhimman ayyuka da kuma taimakon jin kai ga fararen hula a Gaza, da samar da damammakin shiga da isar da kayan agaji, ciki har da kai dauki ga fararen hula a arewacin Gaza da aka yi wa kawanya.

Tun bayan gabatar da wanann daftarin kudiri domin yin shawara a kansa, Amurka ta nuna rashin amincewa da wani batu da ya yi nuni da matakan wucin gadi da kotun kasa da kasa (ICJ) ta dauka, kan bayar da umarni ga gwamnatin Isra’ila, ciki har da dakatar da yakin Rafah, in ji majiyoyi.

A karshe an sake fasali da kuma salon a daftarin, don share duk wata magana kai tsaye game da matakan wucin gadi na ICJ amma an tabbatar da sanarwa da ke mutunta ICJ da ayyukanta a matsyiin kotun adalci da sulhu.

Bugu da kari, daftarin kudurin na karshe bai hada da bukatar Amurka na sake duba zarge-zargen da Isra’ila ta gabatar dangane da alakar ma’aikatan UNRWA da Hamas ba.

Daftarin ya jaddada kare fararen hula, musamman mata, da yara, da kuma wadanda ba mayaka ba. Ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa ‘yan farar hula da kuma duk wani hari dake rutsawa da fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments