Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinu

Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda

Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria.

Wannan daftarin kudurin ya nuna irin yadda duniya ke goyon bayan kafa kasar palasdinu adaidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza, yayin da duniya ke ci gaba da yin tir da cin zarafi da take hakkin dan adam a gazan,

Duk da yake cewa wannan daftarin kudurin ba dole ba ne amma ya kara wa matakin kima a siyasance, kuma ya kara jan hankalin duniya wajen yin matsin lambar diplomasiya kan Isra’ila da kawayenta,  wannan goyon bayan kai tsaye, ya sake mayar da Isra’ila saniyar ware , kuma yasa kasashe duniya yin kiraye-kirayen kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai da kuma kawo karshen yakin gaza .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted