Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu.

Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don warware rikici tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin gargadi

Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don warware rikici tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin gargadi na makonni biyu da malaman jami’ar ke yi.

A sakamakon haka, kwamitocin Majalisar Dattawa kanKwadago da kuma Ilimi mai zurfi za su gana da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da Sakatare-Janar na hukumar Jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a ranar Talata mai zuwa.

. A nasa jawabin kafin taron sirrin, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya ce bukatar kungiyar ita ce gwamnati ta inganta kudaden gudanar da jami’o’i kamar yadda aka amince a yarjejeniyoyin baya. Ya bayyana cewa zuba jari mai dorewa a fannin ilimi ne kadai zai kawo karshen yajin aiki da kuma kara matsayi ga jami’o’in Nijeriya a matakin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments