Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro.
Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya.
Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000.
Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da ake ciki ne na yaki, da kuma tattaunawa matakan da za a dauka a fagen diplomasiyya da kuma hanyoyin tsaro da kare kai.
Ita dai kasar Indiya tana cewa ba za ta taba zama wacce za ta fara amfani da makamin Nukiliya ba, don haka ba za ta zama ta farko da za ta kai wa Pakistan hari ba. Ita kuwa Pakistan ta gina akidarta ta tsaro ne akan cewa za ta iya fara amfani da makamin Nukiliya da Zarar ta faminci cewa wanzuwar kasar tana fuskantar rushewa.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki tukuru domin ganin ta shiga Tsakani da kawo karshen rikicin dake tsakanin kasashen biyu da suke makwabtanta.