Mahamoud Ali Youssouf Ya Zama Sabon Shugaban Kwamitin Gudanarwar AU

An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU. An zabe shi ne a

An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU.

An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar.

Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49.

Dan shekaru 59 da haihuwa, wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Djibouti zai gaji Moussa Faki Mahamat na Chadi wanda wa’adinsa na biyu kan shugabancin kungiyar zai kare a ranar 15 ga watan Maris.

Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta AU sun hada da rikicin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango da Sudan da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na rage taimakon da Amurka ke bayarwa, lamarin da ya shafi nahiyar.

A daya bangaren kuma an zabi Selma Haddadi ‘yar kasar Aljeriya a matsayin mataimakiyar shugaban kwamitin na Tarayyar Afirka.

Ta yi nasara da kuri’u 33 a kan sauran ‘yan takara biyu na Morocco da Masar.

Kungiyar mai kasashe 55 dake wakiltar kusan mutum biliyan 1.5 an dade ana sukarta kan rashin tabaka komai kan matsalolin da suka shafi nahiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments