Shugaban kasar Venezuealla Nicolas Maduro wanda bai dade da yin rantsuwar fara zangon shugabancin kasar a karo na uku ba,ya bayyana cewa:
“ A kasar Venezuela, babu wanda yake son ganin an fada cikin hargitsi, kuma babban aikin da yake a gaban kasar shi ne ‘yanto da dukkanin yankin Latin.”
Shugaba Maduro ya bayyana hakan ne dai a lokacin taron karawa juna sani akan fada da tsarin “Kama-Karya” sannan ya kara da cewa; Muhimman abubuwan da aka gabatar da su a wurin wannan taron, suna nuni da cewa yunkurin rayayye ne, domin a cikin watanni kadan ya watsu a cikin kasashe 77 na duniya.
Haka nan kuma ya yi kira da a samar da wani kawance na kasashe masu fada da tsarin kama-karya irin na Fashiyya- da kuma samar da zaman lafiya da shimfida tsaron demokradiyya da kuma cigaban al’ummu.”