Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa an kawo karshen cutar shan inna, mai nakasa yara a Madagascar.
Tun daga shekara ta 2020, tsibirin ke fuskantar karuwar nau’in cutar shan inna na 1, da har yanzu ke yaduwa.
Wakiliyar UNICEF a Madagascar, Christine Jaulmes, ta yi farin ciki da matakin.
UNICEF ta ce manyan matakan gwamnati, ciki har da hukumomin gargajiya da masu aikin sa kai a kasar ta Madagaska sun taimaka gayan wajen kawar da cutar ta inna ko kuma Polio.
Masu ruwa da tsaki a kasar sun bukaci da kada a yi watsi da matakan da ake dauka na dakile cutar a sahun gaba da kamfen allurer kafin cutar da ake gudanarwa lokaci zuwa lokaci.
A shekarar 2018,ne hukumar WHO ta ayyana Madagascar a matsayin kasar da ta kawar da cutar, kafin ta sake fuskantar cutar bayan shekaru biyu.