A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha.
Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar.
A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama.
A kuma Talatar ne majalisar wakilan kasar ta jefa kuri’ar tsige shugaba Andry Rajoelina yayin wani zama na musamman, duk da cewa shugaba Rajoelina ya riga ya ayyana rushe majalisar.
A karshen watan Satumban da ya shude ne rikici ya barke a kasar, biyowa bayan tsanantar karancin wutar lantarki da ruwan fanfo.
An kuma samu tashe-tashen hankula yayin zanga-zanga, lamarin da ya rikide zuwa ga kiraye-kirayen shugaban kasar ya yi murabus, lamarin da ya tilata mas yin murabus.
Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.