Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa.
Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York.
kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci.
Kasashen Sifaniya da Ireland da Norway su ne na baya-bayan nan da suka nuna amincewarsu a watan Mayun bara da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci, matakin da ya fusata Isra’ila.
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama dai na ganin samar da kasashe guda biyu Falasdinu da Isra’ila shi ne gimshikin samar da zaman lafiya a yankin.