Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza.
Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza.
Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin Netanyahu tare da bayyana ministan harkokin waje Gadion Sa’ir wanda ta ce, ba abinda ya dame shi kamar ci gaba da zama akan kujerarsa, da cewa; Ba ya fahimtar girman musifar da take tunkaro Isra’ila.”
Har ila yau, jaridar ta yi suka ga ministar sufuri Miri Rigiv da cewa saboda ta’annuti, ta ki yin furuci da cewa Isra’ila tana karkashin takunkumin zirga-zirga ta sama, kuma abu ne mai yiyuwa ta fuskanci takunkumi na ruwa.”
Akan ministan ilimi Yoav Kish, jaridar ta ce, babu abinda yake gabansa sai rikicin siyasa akan jami’ar Tel Aviv, maimakon ya mayar da hankali akan yanke alaka da jami’oin duniya su ka yi da jami’o’in Isra’ila.