Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.