London: Zanga-Zangar Neman Kawo Karshen Yaki A Kan

Rahotanni sun ce an gudanar da jerin gwanon ne a birnin Landana daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ire-irensa a kasashe daban-daban
London: Zanga-Zangar Neman Kawo Karshen Yaki A Kan

London: Zanga-Zangar Neman Kawo Karshen Yaki A Kan

An gudanar da gagarumar zanga-zangar neman kawo karshen yakin Amurka da Isra’ila a kan kasar Iran a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Rahotanni sun ce an gudanar da jerin gwanon ne a birnin Landana daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ire-irensa a kasashe daban-daban na nahiyar turai da ma wasu kasashen duniya, domin yin Allah wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila a kan Iran.

Wannan jerin gwanon dai ya kunshi kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma kungiyoyin masu adawa da yaki, wadanda suke fafutuka domin samun zaman lafiya a duniya.

Haka nan kuma sun yi kira da a dakatar da yakin nan take, tare da daukar matakan da suka dace a kan wadanda suka tayar da wannan tarzoma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted