Limamin Juma’ar Tehran Ya Ce Harin Daukan Fansan Iran Ya Karya Kashin Bayan Isra’ila

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a na birnin Tehran ya jaddada cewa: Harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya 2” da Iran ta kai ya karya

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a na birnin Tehran ya jaddada cewa: Harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya 2” da Iran ta kai ya karya kashin bayan makiya yahudawan sahayoniyya

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul-Islam Kazem Siddiqi ya bayyana cewa: Harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya 2” da Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila, hari ne na ilimi wanda ya karya kashin bayan makiya yahudawan sahayoniyya tare da nuna cewa ‘yan mamaya ba za su taba iya yin kuskure ba a kyale su ba.

Ya yi nuni da jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a huduban Juma’arsa da ta gabata cewa: Saddiqi ya cewa: Suna mika jinjina da gaisuwa ta musamman ga shahidi Sayyid Hasan Nasrallah da sakon gaisuwarsu  ga al’ummar Lebanon, kuma suna jaddada tsananin bakin cikinsu kamar su kuma Iraniyawa suna cikin sahun gwagwarmaya tare da jinin shahidansu, sannan suna jaddada cewa suna kan tafarki domin kai wa ga manufa.

Hujjatul-Islam Siddiqi ya kara da cewa: Bayan shahadan jagoran gwagwarmaya Sayyid Hasan Nasrallahi, kamar ruhin ‘yan gwagwarmaya yayi Rauni sakamakon bakin ciki da damuwa, don haka a wannan yanayi suna bukatar rarrashi da bayanan karfafa ruhi da shiryarwa kan irin wannan hali, sakamakon haka Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fito da kansa ya jagoranci sallar Juma’a a irin wannan mummunan yanayi da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments