Limamin  Juma’a Na Tehran Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Al’ummar Musulmi

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau a birnin Tehran  Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammmad Hassan Abu Turabi Fard, ya ce; makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau a birnin Tehran  Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammmad Hassan Abu Turabi Fard, ya ce; makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran suna magana da sauti daya,yayin da juyin juya halin musulunci na Iran ya hada kasashen Lebanon,Yemen, Falasdinu,Iraki da wasu kasashen musulmi.

Limamin na Tehran ya kara da cewa, lokaci ya yi da al’ummar musulmi za su yi watsi da duk wani sabani a tsakaninsu, su dunkule su rika Magana da yawu daya.

Dangane da karatowar watan Ramadan mai alfarma, limamin na Tehran ya ce, watan Ramadan mai alfarma, wata ne na kara kulla alaka da Allah madaukakin sarki da karatun al’kur’ani.

Hujjatul Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma ce; Ma’abota alkur’ani mai girma su ne wadanda aka sani da yin rayuwa ta hankali da ilimi, kuma sakamakon wannan irin raywua shi ne samar da hadin kai da nesantar rabuwar kawuna.

Bugu da kari, limanin na Tehran ya ce hadin kai yana daga cikin sakamakon kare hakkin bil’adama, domin alkur’ani mai girma ya kiraye mu baki daya da mu kasance a tare da gaskiya da kuma tsarin musulunci.

Dangane da abinda Amurk ta mayar da hankali akansa a kiyayyarta da Iran, limamin ya ce  shi ne yakin kwakwalwa da kuma farfaganda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments