A daidai lokacin ziyarar Paparoma Leo na XIV shugaban Katolika na duniya a kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa a hukumance da aka aike masa.
Kungiyar ta yi maraba da ziyarar Paparoma, ta kuma jaddada muhimmancin Lebanon a matsayin kasa mai bambance-bambance na addini da kabilu da akidu, wadda al’ummominta suke bukatar rayuwa tare juna a cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna a zamantakewa da siyasa.
A cikin wannan sakon, Hezbollah ta gabatar da Lebanon a matsayin gada wadda ta hada tsohon tarihi tsakanin Musulunci da Kiristanci da kuma tsakanin al’adu da akidu daban-daban.
Wasikar ta ambaci kalaman Paparoma John Paul II, wanda ya dauki Lebanon ba wai kawai a matsayin gida ba, a’a a ya dauki kasar ne a matsayin daya daga cikin wurare masu tasiri na addinai da aka saukar daga sama.
Hezbollah ta jaddada rawar da kasar ke takawa wajen samar da fahimta tsakanin addinai da al’adu. Wasikar ta nuna cewa rikicin duniya da ya samo asali daga rashin girmama hakkin dan adam, tare da hankoron bautar da shi da kuma tauye masa hakkokinsa, wanda kuma wannan Rashin adalcin ne ya share hanyar kaiwa zuwa ga tashe-tashen hankula da Rashin zaman lafiya a duk inda aka samu hakan.
Wani muhimmin bangare na wasikar ya yi ihara ne ga halin da ake ciki a Falasdinu. Hezbollah ta kira halin da ake ciki a Gaza da “kisan kare dangi a fili” sannan kuma ta bayyana ayyukan Isra’ila a Lebanon shi ma a matsayin “wani zalunci da ba za a yarda da shi ba,” kuma ta dauki wadannan matsalolin a matsayin sakamakon kwadayin gwamnatin Sihiyona na shimfida ikonta a kan albarkatu da filaye na wadannan al’ummomi. Ta kuma jaddada cewa goyon bayan manyan ƙasashe ga Isra’ila a bayyane take haƙƙoƙin al’ummomin yankin ne.
Hizbullah ta kuma nanata alƙawarinta na kasancewa tare da gwamnatin dimokuraɗiyya mai zaman kanta, kiyaye tsaron cikin gida, da kuma fuskantar duk wani zalunci ko mamaye, kuma ta bayyana adawarta da tsoma bakin ƙasashen waje da ke barazana ga ‘yancin kai na Lebanon.
Wasikar ta kuma jaddada abubuwan da suka shafi Musulmai da Kiristoci, kuma ta bayyana mabiyan tafarkin Almasihu a matsayin manzannin zaman lafiya da kare haƙƙin ɗan adam.
Hizbullah ta yi kira ga Paparoma da ya ɗauki matsayi bayyananne wajen nuna Rashin amincwarsa da duk wani rashin adalci da zaluncin Isra’ila a lokacin ziyararsa a Lebanon, da kuma nuna haɗin kai da goyon ga al’ummar Lebanon.
Wasikar ta kammalawa da cewa, Kungiyar Hizbullah na yin fatan alheri da fatan samun nasarar cimma burin tafiyar, na ganin an yada zaman lafiya da karfafa fahimtar juna tsakanin dukkanin Mabiya addinai.