Lebanon : ana zanga zangar adawa da tattaunawar kasar da Isra’ila

A Lebanon ana ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da yunkurin tattaunawar kasar da gwamnatin Isra’ila.
Lebanon : ana zanga zangar adawa da tattaunawar kasar da Isra’ila

A Lebanon ana ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da yunkurin tattaunawar kasar da gwamnatin Isra’ila.

Masu zanga zanagr da dama na alakanta yunkurin tattaunawar da mika wuya cikin sauki ga Isra’ila kwana guda bayan mummunan kisna kiyashin da ta aikata a ranar Larabar da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 300, sannan kuma ta ke ci gaba da kai hare haren kan kasar.

A ranar Talata ne ake sa ran wakilan Lebanon da Isra’ila za su gana da a Amurka.

Wakilan za su gana a birnin Washington, karkashin shiga tsakanin Amurka.

Bangaren Isra’ila ya ce a shirye yake ya tattauna abin da ya kira shawarwarin zaman lafiya da gwamnatin Lebanon.
Sai dai ya ce ba zai tattauna yiwuwar tsagaita wuta da kungiyar Hezbollah ba, tare da cewa zai nemi a kwance damarar kungiyar.

Isra’ila na cewa hare-haren da take kaiwa a ƴan makonnin nan na shafar wuraren da Hezbollah ke da karfi ne kawai, to sai dai hare-haren sama da ta kai sun kashe kusan mutane 2,000, ciki har da yara da mata da dama, da kuma likitoci da ƴan jarida da malamai.

Asibitoci sun cika makil sakamakon yawan wadanda suka jikkata, sannan fiye da mutum miliyan guda ne hare-haren suka raba da matsugunansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted