Lebanon: An Gudanar Da Janazar ‘Yan Jaridari Na Tashoshin Almayadeen Da Almanar
An gudanar da jana’izar ‘yan jarida biyu na tashoshin talabijin na Almayadeen Da Almanar da kuma mai daukar hoto da Isra’ila ta kashe su a lokacin da suke bakin aikinsu na aiko da rahotanni.
Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a kan ‘yan jaridar a lokacin da suke gudanar da aikinsua kudancin kasar Lebanon a wannan Asabar, lamarin da ya yi sanadin shahadar Fatima Fatuni daga tashar Almayadeen da kuma dan uwanta shakiki Muhammad Futuni da ke aikin daukar hoto, sai kuma dan rahoton tashar Alamanr Ali Shu’aib.
Kamar yadda wasu masu aikin agajin gagagwa biyu suka rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin ceton wadannan ‘yan jarida, wadanda su ma jiragen yakin Isra’ila suka kai musu hari.
Shugaban kasar Lebanon Josep Aoun ya yi Allawadai da kakkausar murya kan kisan wadanann ‘yan jarida na kasar Lebanon, tare da shan alwashin daukar matakai na doka domin bin kadun lamari a mataki na kasa da kasa.