A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa.
A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran.
“Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman a isar da wannan ga abokanmu na Iran cewa, Isra’ila tana son ganin an warware wanann takaddama, kuma ba su da niyyar bude wani sabon babi na yaki da Iran,” in ji shi.
Takaddama tsakanin Iran da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kara ta’azzara ne bayan da gwamnatin Sahyoniya ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan Iran a ranar 13 ga watan Yuni wanda ya haifar da yakin kwanaki 12. Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kashe manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliya tare da kashe daruruwan fararen hula a fadin kasar Iran. Ita ma Amurka ta shiga yakin kai tsaye daga bisani, inda ta jefa bama-bamai a wasu cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da