Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem.
Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem a ranar Lahadin da ta gabata. A wajen taron, Larijani ya jaddada goyon bayan Iran ga kasar Labanon da tsayin daka, inda ya yi misali da umarnin Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da goyon bayan gwamnati da al’ummar Iran. Ya jaddada cewa Iran a shirye take ta ba da tallafi ga Lebanon da juriya “a kowane mataki.”
Sheikh Naim Qassem na kungiyar Hizbullah ya godewa shugabanni, gwamnati, da al’ummar Iran saboda irin hadin kai da suka yi da tsayin daka kan zagayowar ranar shahadar sakatarorin Hizbullah, da kuma irin ayyukan da suka yi na nuna goyon baya ga kasar Labanon da tsayin daka.
Ya kuma tabbatar wa da tawagar Iran cewa Lebanon na ci gaba da dagewa wajen fuskantar barazanar Amurka da Isra’ila, tare da jin dadin jama’arta, da ‘yanci, da ‘yancin kai. Qassem ya ce “Duk wanda ya shaida irin jajircewa da hakurin al’ummar Lebanon zai tabbata cewa nasara a kan makiyan Isra’ila nasu ne.”
Shugaban na Hizbullah ya kara da cewa kungiyar na yin hulda da kowa a fili kuma a shirye take ga duk wani nau’i na hadin gwiwa da masu adawa da makiya Isra’ila.
Sheik Naim Qassem ya jaddada cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana barazana ga dukkanin al’ummomi, ma’aikatu da kuma kungiyoyin gwagwarmaya, yana mai mai cewa: “Mun yi imanin cewa fadada burin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila zai gamu da karshen wulakanci ta fuskar tsayin daka na al’ummar musulmi.”