Larijani: Kofar tattaunawa da Amurka a bude take

Ali Larijani, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, hanyar yin shawarwari da Amurka tana nan a bude, duk kuwa da takun

Ali Larijani, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, hanyar yin shawarwari da Amurka tana nan a bude, duk kuwa da takun sakar diflomasiyya da ake yi.

A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X, Larijani ya jaddada cewa “hanyar tattaunawa da Amurka ba a rufe ta ba,” yana mai jaddada cewa Iran “tana bin shawarwari ne na hankali.”

Babban jami’in na Iran ya  nanata cewa Washington na gabatar da bukatu da ke kawo cikas ga tsarin shawarwarin tun daga farko.

Ya kara da cewa, Amurka ta gabatar da batutuwan da ba za a iya cimma matsaya a kansu ba, kamar rage  karfin makamai masu linzami na Iran, inda ya ce wannan da ma wasu batutuwa makamantan hakan ba abu ne da za a iya cimma matsaya a kansa ba.

Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke ci gaba da nuna kyakykyawan fatan da suke da shi kan yiwuwar yin shawarwarin nukiliya da kuma huldar diflomasiyya. Iran ta ci gaba da yin watsi da yunkurin da kasashen yammacin duniya ke yi na dakile shirinta na makami mai linzami, yana mai cewa wannan batu ne da yashafi ‘yancin Iran da kuma batun tsaronta.

Lamarin ya kuma tabo batun  tattaunawa da kasashen turai na  Troika, da vkuma shirinsu na dawo da takunkumin karya tattalin arziki kan shirin nukiliyar Iran.

Bayan sanarwar da E3 suka bayar, majalisar dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da daftarin dokar gaggawa da ke ba da shawarar ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted