Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai.
Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo da kudurin MDD mai amba 2231 da kwamitin tsaro ya fitar da shi a baya. Bugu da kari, wanann siyasar tana a matsayin wani yunkuri ne na yin matsin lamba akan kawancen gwgawarmaya da kuma hana Iran ci gaba a fagagen ilimi da tsaro.
Sai dai duk haka, Dr. Larijani ya ce, wannan irin siyasar za ta mayar da kasashen turai din zama saniyar ware a duniya.
Da yake Magana akan halayyar shugaban kasar Amurka Donald Trump, Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa yana a matsayin wani sabon zubi na Adolf Hitler shugaban ‘yan Nazi a lokacin yakin duniya na biyu.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce, kamar yadda yadda Hitler ya yi mummunan karshe, shi ma Donald Trump abinda zai faru da shi kenan.