Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya

Shugaban kasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa kasarsa ta zama abin misali a duniya, saboda sauyin da jama’a suka bukata tun lokacin

Captain Ibrahim

Shugaban kasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa kasarsa ta zama abin misali a duniya, saboda sauyin da jama’a suka bukata tun lokacin da ya hau mulki a 2022.

“Domin cimma cikakken ‘yancin kai, ya zama dole a bi juyin juya halin inji shi a wani jwabi ta gidan talabijin a jajaribin cika shekaru 65 na samun ‘yancin kai na kasar. Burkina Faso a yau ta zama misali, abin koyi, kuma tana kan hanya madaidaiciya.

Duniya na kallonmu, kuma ba mu da wani zabi illa mu yi nasara,” in ji Traoré. A fannin yaki da ta’addanci, shugaban kasar Burkina Faso ya dage cewa sojojin kasar sun kaddamar da hare-hare masu karfi a cikin shekarar da ta gabata a yankunan da a da ake daukar su a matsayin wuraren da abokan gaba ke iko.

An kwace yankuna da dama a cikin wata guda, inda sojojinmu suka kafa sansani.  “Waɗannan masu laifi waɗanda suka mamaye yankunan ƙasarmu, suna ganin cewa mafakarsu ce, an kore su kuma suna tserewa daga Burkina Faso.

Amma muna gaya musu cewa yanzu suna da zaɓi biyu kawai: su gudu daga Burkina Faso ko su mutu saboda sojojinmu suna kan daga. Traoré ya yi kira ga mutanen Burkina da su hadu waje daya don tunkarar kalubalen da suka shafi ci gaban kasar, musamman masana’antu da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa don amfanin al’ummar kasar baki ɗaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted