Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza

A wani lokaci yau Litini ce kwamitin tsaro na MDD, zai kada kuri’a kan daftarin kudirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump na Amurka

A wani lokaci yau Litini ce kwamitin tsaro na MDD, zai kada kuri’a kan daftarin kudirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump na Amurka kan Gaza.

Kafin hakan Amurka ta sha matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da daftarin kudurin na Trump.

Amurkar da wasu kawayenta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin wanda ya amince da shirin zaman lafiya na Donald Trump kan Gaza.

Qatar, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Indonesia, Pakistan, Jordan, da Turkiyya sun bayyana goyon bayansu ga daftarin kudurin na Amurka wanda ya tanadi kafa kwamiti da zai kula da gwamnatin rikon kwarya a Gaza da rundunar kasa da kasa a yankin Falasdinu, tare da fatan amincewa da shi cikin sauri,” in ji su a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.

A ranar Alhamis, Amurka ta yi gargadi game da hadarin rashin amincewa da daftarin kudurin, Yayin da kasashen Larabawa ke nuna fargabar darewar yankin falasdinun gida biyu.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da wasu daga cikin ministocinsa sun sake nanata adawarsu ga kafa kasar Falasdinu kafin kada kuri’ar da za a yi yau Litinin kan daftarin kudurin kan Gaza, wanda ke nuna yiwuwar samar da kasar Falasdinu a nan gaba.

Kungiyoyin Falasdinawa sun yi watsi da daftarin kudurin wanda kuma ya tanadi shawarar tura dakarun kasashen waje kusan 20,000 zuwa Gaza, suna kira ga Aljeriya, wacce ba memba ce ta dindindin a kwamitin Tsaron, da ta yi watsi da shi.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments