Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi.
Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da ake bukata don ganin kasar Iran ta fice daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman Nukliya saboda kasashen Turai sun maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa kasar.
A cikin makon da muke ciki kasashen turai guda uku Faransa, Jamus da kuma burtania suka yi amfani da wani abu da ake kira snapback da ya zo cikin yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar iran wanda kasashen 5+1 suka cimma da kasar a shekara ta 2015. Sai Amurka ta fice daga yarjeniyar, kasashen turai uku kuma suka sabawa yarjeniyar kasashen Rasha da china da kuma ita Iran ne kawai suka rage a cikin ta.
Amma bayan yakin kwanaki 12 da Amurka da HKI suka kaiwa Iran suka kuma kasa kaiwa ga bukatunsu kan kasar , sai wadannan kasashen uku, wadanda suka yi watsi da yarjeniyar kusan shekaru 10 da suka gabata suka zo suka yi amfani da abinda ake kira tnapback a cikin yarjeniyar don dawo da dukkan takunkuman MDD kan kasar Iran bayan an dauke su.