Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani zama na gaggawa a jiya Talata, domin tattauna mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza, inda ya mayar da hankali musamman kan fursunonin Isra’ila da ke hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinu.
A tsakiyar zaman dai batutuwa biyu ne suka dauki hankali: daya daga kasashen yammacin turai don ba da fifiko kan batun sakin fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su, da kuma wani wanda ke samun goyon bayan kasashe da dama, wanda ke nuni da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a kan Falasdinawa sama da miliyan biyu da aka yi wa kawanya.
Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Turai, Asiya ta Tsakiya da Amurka, Miroslav Jenca, ta bude taron da yin gargadi mai tsauri: matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na tsawaita ayyukan soji a daukacin Zirin na haifar da babban hadari ga fararen hula Falasdinawa da Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su.
Jenca ta yi Allah-wadai da “tashin hankalin da ke ci gaba da faruwa,” ciki har da kisa da nakasa mutanen da ke neman abinci, tana mai nanata cewa, hana fararen hula samun agaji na abinda zai ceci rayuwarsu kamar abinci da Ruwan sha da gangan, hakan yana a matsayin laifin yaki ne.
Ta bukaci a bude dukkanin hanyoyin isar da kayan agaji cikin gaggawa ba tare da kawo wani tarnaki ko cikas ga wannan shiri ba, da kuma daukar matakan tattaunawa da gaske wadda zata kawo karshen zubar da jini a Gaza.