Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA

Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin

Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA

Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka kare, za a dakatar da aiwatar da tsare-tsare da yarjejeniyoyin da aka kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Sakatariyar kwamitin tsaron kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, bayan yarjejeniyar da aka rattabawa hannu tsakanin Seyyed Abbas Araqchi da Rafael Grossi. An yi wannan bayani ne dangane da tsare-tsare da ministan harkokin wajen kasar da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka rattabawa hannu dangane da tsarin mu’amala tsakanin Iran da IAEA bisa la’akari da sabbin yanayi da ake ciki bayan hare-haren soji da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan cibiyoyin makamashin nukiliya na kasar Iran bisa tsarin kariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments