Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke a baya.
Babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya ziyarci rundunonin sojoji a yankunan Isfahan, Tabriz, da Hamadan. A yayin da yake yin nazari kan shirye-shiryen wadannan runduna tare da rakiyar kwamandoji, mayaka, da matukan jirgin sama, ya lura da tsayin daka da al’ummar Iran suka yi wajen tunkarar wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar na tsawon kwanaki 12. Ya ce: Dukkanin Iran tun daga sojojin kasa da sojojin tsaron sararin samaniya da dakarun sa-kai kai na Basij, da dakarun kare juyin juya halin Musulunci, da sauran al’umma, su ne jigon yakin da aka yi a baya-bayan nan, kuma suna fada da gwazo da dukkan karfinsu, ta yadda Jamhuriyar Musulunci za ta ci gaba da kasancewa abin alfahari a tarihi.
Babban kwamandan ya ci gaba da cewa: Batun makamashin nukiliyar Iran shi ne babban jigon makiya, to amma abin da suka yi a fagen daga ya sha bamban da da’awarsu ta farko, kuma sun nuna cewa sun aiwatar da wani sahihin tsari a kan al’ummar kasa da kuma tsarin kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to amma bisa godiyan Allah, hubbasar da al’ummar Iran suka yi sun yi nasarar rusa dukkanin makirce-makirce makiya.