Kwamandan sojan Iran Amir Hatami wanda ya gana da kwamandan dakarun kare juyin musulunci Janar Muhammad Pakpour saboda tunawa da makon hadin kai, ya kara da cewa; Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran da al’ummarta sun fara aiki tukuru domin kare cikakken ‘yancin Iran.”
Har ila yau, Amir Hatami ya yi ishara da hadin gwiwa a tsakanin sojojin da dakarun kare juyin juya halin yana a matsayin ginshikin tsaron kasar Iran, kuma wata kofa ta kai wa mataki na koli na tsaro.
A gefe daya dakarun kare juyin musulunci ( irgc) sun jaddada matsayarsu ta ci gaba da zama cikin Shirin fuskantar abokan gaba.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun 1980-1988, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun jaddada cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafi da makiya za su yi, za su fuskanci mummunan martani da zai zame babban darasi a gare su.
A cikin bayanin da suka yi na farkon makon tsaro na dakarun IRGC sun bayyana cewa: A hakikanin gaskiya makon tsaro, biki ne na nasarar gwagwarmayar jama’a, kuma abin tunawa na daya daga cikin manyan abubuwa mafiya haske a tarihin juyin juya halin Musulunci, sannan abin alfahari ga kasar, kuma abin alfahari ne a duniya. Sannan tsaro mai alfarma wani zamani ne da al’ummar Iran bisa dogaro da imani da hadin kai da jagorancin Ubangiji suka samu nasarar dakile duk wani yunkuri na gaba daya da makiya da suka shirya a kan iyakokin kasar Iran da juyin juya halin Musulunci da tsarin Musulunci da kuma kiyaye martaba da ‘yancin kai da cikakken yankin kasar daga makircin masu girman kai.