A kwana uku na fadan da ake yi a garin Suwaida’a a kasar Syria, an kashe mutanen da sun kai 100, yayin da wani adadin mai yawa su ka jikkata.
Majiyar tsaro daga kasar ta Syria ta ce a daren jiya an yi fada mai tsanani a tsakanin ‘yan Duruz, da kuma kabilun larabawan daji a yankin filin saukar jiragen saman a “Sa’alah”.
Tashar talabijin din “Suwaidah 24′ ta ce an fadin ne a fagage 4 da su ne, Hazm, Kanakar, Ta’arah, da kuma filin saukar jiragen saman a Sa’alah.
An rika jin karar manyan bindigori da fashewar bama-bamai a garin Kanakar.
A gefe daya jami’an tsaron kasar ta Syria sun sanar da shiga cikin yankuna biyu da zummar tabbatar da tsaro.
Asibitocin yankin sun sanar da cewa a cikin sa’oi 24 da su ka gabata sun karbi gawawwakin mutane 50 da kuma wasu 200 da su ka jikkata.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Marsad” ta sanar da cewa; adadin wadanda su ka rasa rayukan nasu ya karu zuwa 99, daga cikinsu da akwai kananan yara da kuma mata biyu;
Tun da fari, majiyar gwamnatin kasar ta Syria ta ce, ta aike da jami’an tsaro ne domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Su kuwa shugabannin addini a yankin sun yi kira da a tsagaita wutar yaki.