Kungiyar wasan Kareti ta Iran ta zama ta daya a nahiyar Asiya, yayin da Iraki ta zo ta biyu sai kuma Tajikistan ta uku.
An yi wannan gasar ne ta Asiya a garin Calus dake Arewacin Iran wanda ya sami halartar kasashe da dama. Daga cikin kasashen da su ka shiga gasar wasannnin da akwai Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman sai kuma Tajikistan.
An bude wannan gasar ne dai daga ranar 19 ga watan nan na Febrairu, kuma za a rufe ta zuwa gobe 22 gare shi.
Da akwai ‘yan wasa 120 na cikin gida da waje da su ka shiga cikin gasar, da ‘yan kallo 700 a cikin dakin wasa.