Kungiyar Tarayyar Turai EU Ta Mika Bukatunta Ga Kasar Iran.

Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita

Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi a matsayin mara inganci,

Iran a matsayinta na member a NPT ta yi aiki da nauyin da ya rataya akanta, karkashin yarjejeniyar JCPOA yayin da Iran ke jiran kungiyar tarayyar turai ta yi aiki da abin da ya hau kanta kuma ta cire takunkumi, amma hakan bai samu ba, kasashen turai da hadin bakin Amurka suna barazanar sake dawo da takunkumai don matsin lamba ga kasar Iran ta bada kai bori ya hau.

Kallas ta bayyancewa dole ne kasar Iran ta bada cikakken hadin kai ga hukumar IAEA, ta ba wa wakilanta damar bincika a cibiyoyin nukiliyarta ba tare da bata lokaci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted