Kungiyar Red Crescent Ta Iran Ta Jajanta Kan Gobarar Daji A Los Angeles

Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ya nuna juyayi ga wadanda gobarar daji ta Los Angeles ta shafa tare da bayyana shirin IRCS

Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ya nuna juyayi ga wadanda gobarar daji ta Los Angeles ta shafa tare da bayyana shirin IRCS din na aika kayan agaji.

Iran ta bayyana shirinta na aikewa da agajin jin kai domin taimakawa gobarar daji a Los Angeles.

shugaban kungiyar Pirhossein Kolivand, a cikin wata wasikar ta’aziyya ga Cliff Holt, shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta Amurka, ya bayyana shirin aikewa da agajin jin kai zuwa Amurka, a matsayin taimakawa bala’in da ake fama da shin a gobara a kudancin California.

Rahotannin sun ce akwai akalla wurare shida da har yanzu gobarar ke ci a fadin gundumar Los Angeles.

Akalla mutane 16 ne suka mutu, yayin da jami’ai suka yi gargadin cewa ba za’a san adadin na gaskiya ba har sai an gama bincike a wuraren da lamarin ya shafa.

Ya zuwa yammacin ranar Juma’a, kimanin mutane 100,000 ne ake kwashe a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments